
Daga BELLO A. BABAJI
Jami’an rundunar ƴan sandan farin kaya, DSS a Edo, sun kama wani ɗan fafutukar ƴanci kuma jagoran Majalisar Talakawa ta jihar, wato Kwamared Kola Edokpayi a Benin, babban birnin jihar bisa shirya gangamin nuna goyon Shugaban mulkin soja na ƙasar Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traore.
Rahotanni sun bayyana cewa, an shirya gudanar da gangamin ne a wasu ƙasashen Afrika da suka haɗa da Ghana da Afirka ta Kudu da sauran su.
Duk da cewa, Edokpayi ya gana da Kwamishinan ƴan sandan jihar kwana kafin ƙaddamar da gangamin, inda suka amince da janye batun, daga bisani a ranar jami’an DSS da na ƴan sanda suka je ofishinsa tare da kame mutane shida.
Baya ga haka ne aka sako mutane huɗu daga ciki, inda Edokpayi da wani mamba suka cigaba da zama a hannun hukumar.
Lamarin da ya haddasa nuna fushi daga ƙungiyoyin ƴancin ɗan-adam masu zaman kansu da wasu ƙungiyoyin al’umma a Nahiyar Afirka, kasancewar suna ganin hakan a matsayin yunƙurin tauye masa ƴanci.
Ƙungiyar Take It Back (TIB) reshen Edo, ta nemi a gaggauta sako jagoran, ta na mai bayyana hakan a matsayin abinda aka yi ba bisa doka ba.
