Ruwa na taimaka wa ƙoda wajen tace jini da samar da fitsari

Spread the love

Tare da CHIROMA AMINU ASID

Ruwa yana da muhimmancin gaske ga lafiyar ɗan adam, musamman wajen taimaka wa lafiyar ƙoda wajen tace jini da samar da fitsari (urine formation), saboda ƙoda tana samun sauƙi wajen wanke jini da tace datti daga cikin jini idan da akwai isasshen ruwa ajikin mutum, rashin wada taccen ruwa acikin jinin mutum yana sa fitsarin mutum yazama kadan sannan yasanja launin kala zuwa baki (very dark yellow or amber), wanda hakan yana nuni da rashin wadatuwar ruwa ajiki (dehydration), kasan tuwar hakan yana bawa ƙoda tsaiko wajen tace datti da gubar da jiki yake samarwa.

Masana kiwon lafiyar ƙoda sun bayar da shawarar shan tsaftacaccen ruwa akalla lita 2 zuwa 3 (8-12 cups) a ko wace rana, a takaice lita 2 zuwa 3 shine mafi karanta na ruwan da mutum yakamata yasha a rana, saboda haka shan ruwa samada lita 2 zuwa 3 karin alfanu ne ga lafiyar ƙoda musamman a lokacin zafi.

Shan isasshen ruwa na taimaka wa aikin ƙoda wajen wanke ko tace jini da ruwan jiki daga guba da sauran muggan sinadaran da jiki ke samarwa domin fitar dasu zuwa cikin fitsari.

Bugu da kari, yawan fitar gumi na nuni da yawan ruwan dake fita daga jiki, kuma yawan gumin daya fita na nuni da karanchin fitsarin daza’a samu, dan haka inkayi gumi sosai ta hanyar motsa jiki ko yawo cikin rana hakan zaisa karasa ruwa mai yawa ajikin ka domin gujewa faruwar hakan sai ka yawaita shan ruwa akai akai, kada kadamu da yawan yin fitsari dayawa inde kasan yawan shan ruwan da kakene ya kawo shi.

Saboda haka, rashin shan isasshen ruwa nada hadarin gaske domin yana haifar da dunkulewar sinadaran dake cikin fitsari har daga karshe ya haifar da tsakuwar ƙoda (kidney stones), ciwon tsakuwar ƙoda na iya tilasta yin tiyatar ƙoda domin cire tsakuwar.

A shawarce, Yana da kyau mu riƙa yawan shan ruwa musamman a irin wannan yanayin da muke ciki na zafi, saboda mu na rasa ruwa mai yawa daga jikin mu wanda hakan yakesawa muke yin fitsari mai zafi sakamakon rasa ruwan da mukeyi ajikin mu.Ruwa rayuwa ne!

Daga ɗan uwanku, Chiroma Aminu Asid

By ukarofi