Nijeriya ta yi asarar biliyan N1.3 ga cutar Ebola ta tumatur a jihohi uku

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Niueriya ta ce kawo yanzu Nijeriya ta yi asarar sama da Naira Biliyan 1.3 sakamakon ɓarkewar cutar tumatur, wanda da aka fi sani “Ebola Tumatur” a jihohi uku.

Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a taron ƙara wa juna ilimi na kwanaki huɗu da ake gudanarwa a cibiyoyin hada-hadar kuɗi a ranar Laraba a Abuja.

HortiNigeria ne suka shirya taron bitar tare da hadin gwiwar Nigeria Incentiɓe-Based Risk Sharing System for Agricultural Lending Plc.

Kyari ya ce, sakamakon ɓullar cutar ta sa kwandon tumatur mai nauyin kilogiram 50 ya tashi daga Naira 5,000 zuwa Naira 10,000 da kuma kusan Naira 30,000, wanda hakan ya ta’azzara hauhawar farashin kayayyaki da kuma taɓarɓerewar kasafin kuɗin gida. A cewarsa jihohin da aka samu asarar sun haɗa da Kano, Katsina da kuma Kaduna.

Ya bayyana cewa, cutar ebola ta tumatur ta nuna gazawar tsarin noma a ƙasar, inda ya ƙara da cewa kwarin da ke damun tumatur na iya lalata amfanin gonar tumatur cikin sa’o’i 48, wanda hakan zai haifar da mummunar asarar amfanin gona.

A cewarsa, wannan rikicin ya nuna buƙatar gaggawar samar da dabarun yaƙi da kwari, da zuba jari a irin nau’in amfanin gona mai jure wa da kuma haɓaka tallafi ga manoma domin kare sarƙar samar da abinci a ƙasar.

Ya ce, “Tumati da barkono, kayan abinci masu muhimmanci a kusan kowane gida a Nijeriya, su ne kayan abinci na yau da kullum don dafa abinci.

“Lokacin da farashin waɗannan kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabi, sai sun shafi dukkan kayan abinci.

By ukarofi