Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau
Ƙaramin Ministan Tsaro, Dakta Bello Mohammed Matawallen, ya jajantawa al’ummar Maru bisa kisan babban Limamin Masallacin Juma’a na Maru, Alƙali Salihu Suleiman wanda wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai suka kashe tare da ‘ya’yansa guda biyu da suka yi garkuwa dasu watanni biyu da suka wuce.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na jihar Yusuf Idris ya rabawa manema labarai ranar Juma’a.
Matawalle ya kuma bayar da tallafin tsabar kuɗi naira Miliyan biyar, buhunan shinkafa guda 10, katon spaghetti guda 10 da kuma katon macaroni 10 ga iyalan mamacin.
Ya koka da yadda ‘yan bindigar ke ɗaukar wani sabon salo a jihar inda a yanzu ake kai wa malaman addini hari.
Matawalle ya bayar da tabbacin cewa ma’aikatar sa za ta ci gaba da tura ƙarin jami’ai a jihar domin kawar da masu aikata laifuka gaba ɗaya.
A cewarsa gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana ɗaukar duk matakan da suka dace domin kawo ƙarshen ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.
Ministan ya ci gaba da bayanin cewa shugaban ƙasar ya baiwa sojoji dukkan kayan aikin da ake buƙata, kuma nan ba da jimawa ba, za su tabbatar da dawowar zaman lafiya a yankin.
Ya yi kira ga ‘yan ƙasar da su taimaka wa jami’an tsaro da sahihin bayanan sirri domin samun nasara a yaƙin da ake yi da ‘yan ta’adda da sauran miyagun laifuka
Ya ce tsaro na buƙatar goyon bayan duk wani ɗan ƙasa mai kishin ƙasa ba tare da la’akari da siyasa ko addini ba.
Ministan ya samu wakilcin Sakataren Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara, Hon. Ibrahim Umar Ɗangaladima yayin ziyarar .
Matawalle ya jaddada buƙatar haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohin yankin Arewa maso Yamma da gwamnatin tarayya domin kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci da kuma munanan ayyukan.
Da yake karbar tawagar, ɗaya daga cikin iyalan marigayin kuma Sarkin Maru, Alh Abubakar Gado Maigari ya gode wa ministan bisa yadda yake nuna damuwarsa ga al’ummar jihar a koda yaushe, ya kuma yi addu’ar Allah ya ci gaba da saka masa, ya yi masa jagora, ya kare shi, da kuma tallafa masa a dukkan harkokinsa.
