Kwara: Sojoji sun kama ƴan ta’adda 12

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kimanin mutane 12 ne Sojoji suka kama bisa zargin su da hannu a ayyukan ta’addanci na tsagin kungiyar Boko Haram da ake kira da Mahmuda, wanda ya mamaye yankin ‘Kanji Lake National Park’ da ke iyakokin Jihohin Neja da Kwara.

Kungiyar, kafin yanzu ta addabi al’ummar kauyukan da ke kewayen yankin da hare-harenta a Kananan Hukumomin Baruten da Kaiama a Jihar Kwara da Borgu a Neja.

Babban Jami’in Shiyya ta 2 (GOC), Manjo-Janar Obinna Onubogu, wanda ya ziyarci sansanoni a Kaiama da Baruten, ya bayyana hakan a lokacin da ya ke karbar ba’asi game da halin tsaro a yankin, ranar Asabar.

Ya ce, an kama mutane sha biyun ne da ake zargi a wurare mabanbanta a yankin Kanji Lake National Park da garuruwan dake kusa da shi.

Haka kuma, an tabbatar da cewa biyu daga cikinsu ƴan kungiyar ta’addancin ne yayin da sauran kuma sun kasance masu taimaka musu ne wajen aikata manyan laifuka.

GOC’n ya shaida wa manema labarai cewa, tawagar jami’ansu suna aiki tukuru wajen ganin sun dawo da zaman lafiya da tsaro mai ďorewa a yankin domin walwalar al’umma.

Ya ķara da cewa, jami’an a yayin atisayensu sun kutsa har na tsawon kilomita 90 daga Kemanji zuwa dajin Kanji inda a nan ne asalin sansaninsu ya ke.

Har’ilyau, ya bayyana cewa jami’an a yayin hakan sun yi nasarar tarwatsa ƴan ta’addan da wasu hanyoyin aikata manyan laifuka a yankunan.

By Babaji