Borno: ‘Yan Boko Haram sun halaka sojoji da garkuwa da wasu a wani farmaki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wasu mahara da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne, sun farmaki wani sansanin sojoji a Karamar Hukumar Marte dake Jihar Borno, inda suka kashe wani adadi na sojoji.

Majiyoyi daga mazauna yankin da jami’an tsaro sun tabbatar da aukuwar lamarin, inda suka ce ya faru ne a sansanin jami’an Task Force na Bataliya ta 153 da misalin karfe 3:00 na dare, ranar Litinin.

Wani shaida da ya nemi a sakaye sunansa ya ce, an tarwatsa sojojin da yin garkuwa da da dama daga cikinsu a yayin farmakin.

Ya ce, mayakan ISWAP sun karbe iko da Marte yayin da wasu sojoji suka tsere zuwa Dikwa, waɗanda suka fake a Birget na 24 na jami’an Task Force.

Ya kuma ce, mayakan sun ƙone tankokin yaki tare da debe makamai da alburusai daga sansanin.

Marte Karamar Hukuma ce da ke da nisan kilomita 38 daga Dikwa, wato Hedikwatar Karamar Hukumar Dikwa a jihar.

Wani shaida a Dikwa ya fada wa wakilinmu cewa an jiyo harbe-harben bindigogi da hango shawagin jirgin sama na yaki na Sojojin sama a yankin.

By Babaji