Sojoji sun kashe ƙasurgumin dan bindiga a jihar Taraba

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar 6 Brigade, Sashe na 3 dake aiki a ƙarƙashin rundunar ‘Operation ‘Whirl Sroke (OPWS) sun kashe ɗan bindiga ɗaya kuma sun ƙwato makamai a jihar Taraba.

Mataimakin shugaban hulɗa da jama’a na rundunar Olubodunde Oni ya sanar da haka ranar Laraba a garin Jalingo.

Oni ya ce dakarun sun yi bata-kashi da maharan a hanyar Bandawa zuwa Karim Lamiɗo.

Ya ce jami’an tsaron sun samu nasarar kashe ɗaya daga cikin maharan inda sauran suka gudu.

“Jami’an tsaron sun kwato bindiga daya kirar AK-47 da harsasai 39.

Daga nan kwamandan rundunar Kingsley Uwa ya bayyana yadda rundunar ta taimaka wajen sasanta rikicin dake shirin ɓarkewa tsakanin mazaunan ƙauyen Kashimbilla dake ƙaramar hukumar Takum a jihar Taraba da mazaunan ƙauyen Jato Aka dake ƙaramar hukumar Kwance dake jihar Benuwe.

Uwa ya ce rundunar ta yi haka ne bayan zaman da ta yi da masu ruwa da tsaki na ƙauyukan inda suka tattauna hanyoyin da suka fi dacewa wajen samar da zaman lafiya a ƙauyukan.

By ukarofi