Kano: An kama awakai bisa lalata bishiyoyi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Faruwar wani al’amari ya jefa al’umma cikin al’ajabi a Kano yayin da Ma’aikatar Kula da Muhalli da Sauyin Yanayi ta fara kamen awakan da ke lalata bishiyoyi, wanda hakan ke haifar da koma-baya ga ayyukan raya birane a jihar.

Kwamishinan Ma’aikatar, Dakta Dahir M. Hashim ya tabbatar da hakan a wata takarda, ranar Juma’a, inda ya ce tuni aka kai wasu awakai ofishin rundunar ƴan sanda bayan sun lalata wasu bishiyoyi da aka shuka a wasu manyan tituna.

Ya ce, a kokarinsu na raya birane, sun shuka bishiyoyi a manyan titunan ne domin rage matakin zafi da ďumamar yanayi gami da ķawata ƙwaryar birnin jihar.

Ya bayyana cewa, yunķurin nasu yana fuskantar kalubale daga awakan da ke gararamba acikin gari, inda suka samu korafin cewa awakan na lalata bishiyoyin, lamarin da ya sa suka fara kamen.

Kwamishinan ya kuma ce, jami’ansu suna cigaba da kula da al’amarin, yana mai kira ga al’umma da su bada goyon baya wajen kula da muhallansu don tabbatar da yanayi mai kyau a Kano.

By Babaji