Ƙaddamar da littafi: Sule Lamiɗo ya buƙaci Tinubu ya biya bashin biliyan N45 da Abiola ke bin Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A karo na goma sha uku, tsohon magatakardan jam’iyyar SDP ta ƙasa, kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da ya warware bashin kwangilar Naira Biliyan 45 da wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993, Bashorun Moshood Kashimawo Abiola ke bin Nijeriya.

Yin hakan, ya ce faɗa wa Tinubu, zai warware batun 12 ga watan Yuni baki ɗaya.

Sule Lamido ya faɗi hakan ne a littafin tarihinsa da ya rubuta mai suna “Being True to Myself”wanda aka ƙaddabar ranar Talata a Abuja.

Littafin mai shafi kimanin 500 ya mayar da hankali ne kan rayuwar marubucin tun daga ƙuruciya har zuwa gwagwarmayar siyasarsa daga jamhuriya ta biyu kawo yanzu.

A wani babi mai taken “Matsayata kan rushe zaɓen 12 ga watan Yuni”, Sule Lamido ya musanta dalilin da tsohon shugaban Nijeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayar a littafinsa mai suna “A Journey in Serɓice” a matsayin dalilin da ya sa ya rushe zaɓen watan Yunin 1993.

Bayan kammala ƙaddamar da littafi, marubucin ya yi ƙarin bayani dangane da haƙiƙanin abin da yake nufi a babin.

Ya ce, “a littafin Babangida ya ce Abiola shi ya ci zaɓe. A gaskiya shi ne ya ci zaɓen. Yanzu hujjar sokewa kuma wani abu ne daban.

“Amma ni abin da ya gaya min cewa shi ne dalilin da ya sa ya soke zaɓen shi ne saboda Abiola yana bin Nijeriya bashi kuɗi naira biliyan 45,000 saboda haka idan ya ba shi wannan mulki to zai amfani da mulkin ya biya kansa kuma a lokacin nan ƙasar ba ta da wannan kuɗin da za ta biya shi, shi ya sa ya soke zaɓen.

“Kenan Abiola ya ci zaɓen amma an zalunce shi an hana shi sannan kuma ga kuɗi yana bi ba a biya shi ba. Idan ana so a yi adalci tunda mutumin nan ya mutu to kuɗin da yake bi naira biliyan 45,000 kamar yadda Babangida ya gaya min shi ya sa ya soke zaɓen nan, to a ba wa iyalan Abiola, a biya su kuɗinsu. Shi kenan daga nan komai ya ƙare kenan.”

“Shi ya sa nake faɗa wa Tinubu cewa ya kamata maganar June 12 a ƙare ta. Saboda haka a biya wannan bashin na naira biliyan 45,000 ga iyalansa. Shi kenan magana ta ƙare,” inji Sule Lamido.

By ukarofi