Gwamnan Kano zai jagoranci alhazan jihar zuwa aikin hajjin 2025

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa zai raka alhazan jihar Kano a aikin hajjin 2025 a ƙasar Saudiyya.

Jaridar Independent Mirror ta ruwaito cewa, da yake magana a lokacin wani taron gabanin aikin Hajji a Kano, ya ce aikin hajji, aikin ibada ne da ke buƙatar girmamawa da nuna ɗa’a”.

“Wannan ba tafiya ce kawai ba, ibada ce, ni da kaina zan jagoranci alhazan Kano don tabbatar da an gudanar da aikin Hajji cikin kwanciyar hankali” inji shi.

A cewar mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, Yusuf ya kuma bayyana shirin tallafawa alhazai na 2025. Waɗannan sun haɗa da ƙarin jami’an da za su taimaka wa alhazai tun daga isowarsu zuwa zamansu a wurare daban-daban a ƙasar Saudiyya.

“Mun tattara tawagogi masu kwazo domin biyan buƙatun alhazanmu—daga filin jirgin sama zuwa masauki, da kuma tsawon zamansu a ƙasar Saudiyya, burinmu shi ne mu sanya aikin hajjin bana ya zama mafi sauƙi da kwanciyar hankali a tarihin Kano,” inji Gwamnan.

Ya kuma ce maniyyatan su kasance masu kyakykyawan hali, musamman matasa da mata, kuma su mutunta kimar Kano.

“Ga matasan mu, ina kira gare ku da ku guji duk wani abu da zai iya zubar wa jiharmu da kima, su kuma matanmu ku tuna cewa matan Kano an san su da mutunci, ku wakilci mu da alfahari, ku mutunta kanku, da kare martabar al’adunmu da addininmu,” inji shi.

Ya kuma yi gargaɗi game da shan muggan kwayoyi da lalata, yana mai cewa hakan ya saɓa wa manufar aikin Hajji da koyarwar Musulunci.

Yusuf ya kuma yi magana game da tsafta da tarbiyya, ya ce, “Tsafta wani ɓangare ne na imani, ina roƙonku da ku kiyaye ɗakunanku da muhallinku yayin da ku ke Saudiyya.

By ukarofi