Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Wani gogaggen ɗan kasuwa kuma jajirtaccen ma’aikacin gwamnati, Alhaji Sa’idu Isma’il Koya, ya yaba wa ƙungiyoyi biyar na matasa bisa ba shi lambar yabo da suka yi saboda sadaukarwarsa wajen hidima ga al’ummar.
A yayin taron karramawar da ya gudana a dakin taro na Sultanes Suit Kano, Koya ya bayyana cewa matasa su ne ginshikin kowace al’umma, yana mai cewa tallafa musu na nufin taimakawa ɗan Adam ne gaba ɗaya.
“Na yi matuƙar farin ciki da samun wannan lambar yabo. Ni dai ina aikina ne kawai, amma ashe mutane suna jin daɗin hidimar da muke yi musu, wannan zai ƙarfafa ni in ƙara jajircewa,” inji Koya.
Ya buƙaci sauran ’yan kasuwa a jihar da su ci gaba da tallafawa marasa ƙarfi da masu buƙata a cikin al’umma.
A nasa jawabin, shugaban Youth Ambassadors of Nigeria, Kwamared Tijjani Abdulmumin, ya ce sun baiwa Alhaji Sa’idu lambar yabo ne bisa la’akari da tarihin ayyukansu na hidima ga jama’a a cikin Jihar Kano Jigawa.
“Lambar yabo ta bani ta muka miƙa ta cikin alfahari ga Alhaji Sa’idu Isma’il Koya, wanda shi ne shugaban kamfanin Koya Motor’s and Construction Nigeriya Limited kuma gogaggen ma’aikacin gwamnati ne kuma da ɗan kasuwa, taken kyautar shi ne ‘Zakaran Cigaban Al’umma’ domin girmamawa bisa gagarumar gudunmawar da ka bayar wajen cigaban al’umma, taimakon jama’a, cigaban matasa da kuma hidima ga ƙasa,” inji Kwamared Tijjani.
Ya ƙara da cewa, “Jagorancinka da himmarka wajen aiki abin a yaba ne ƙwarai da gaske; ka jajirce, ka yi sadaukarwa domin amfanin duk wanda ya haɗu da kai. Alhaji, tasirin alherinka ga rayuwar mutane da kungiyoyi da al’umma gaba ɗaya, da kuma yadda ka baiwa matasa da ɗalibai ƙwarin gwiwa da horo ya sanya ka cancanci zama Jakadan Zaman Lafiya. Mu a shugabancin YAN muna alfahari da kai, muna addu’a Allah ya ba ka lafiya, ƙarfi da tsawon rai domin ka ci gaba da aikinka na alheri ga ɗan Adam,” inji shugaban.
ƙungiyoyin da suka bada wannan karrawar sun haɗa da Jigawa State Young Politician Forum da African Uniɓersal Youth Consultatiɓe Forum da United Nigerian Youths da Young Ambassadors of Northern Nigeria YAN.
Taron dai ya samu halartar ɗalibai matasa maza da mata daga Kano da kuma Jigawa.
ƙungiyoyin dai sun sha alwashin ci gaba da karrama waɗanda ke bada gudunmawa wajen ci gaban al’umma.
