Kogi: Iyalan sarkin da aka yi garkuwa da shi na neman taimakon rabin kuďin fansa bayan tara miliyan N25

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Iyalan Oba Dada James Ogunyanda, wanda aka yi garkuwa da shi a makon da ya gabata, sun roƙi gwamnati da ķungiyoyin al’umma da ɗaiɗaikun jama’a da su taimaka wajen samar da Naira miliyan 50 da ƴan bindiga suka bukaci a biya a matsayin kuďin fansa ga sarkin.

An yi garkuwa da shi sarkin ne na ķauyen Okoloke dake Karamar Hukumar Yagba ta Yamma na Jihar Kogi da misalin ƙarfe 2 na dare inda aka tilasta shi zuwa wani boyayyen waje.

Wata majiya daga fadar sarkin ta ƙaryata rahoton da ke cewa an cimma matsaya da ƴan bindigar akan a biya miliyan N12, inda ta ce a matsayinsu na iyalansa sun yi ƙoƙarin tara Naira miliyan 25 zuwa ranar Lahadi, amma ƴan bindigar sun ce sai an biya su miliyan N50.

Da farko miliyan N100 ne suka buƙaci a biya su, tana mai cewa ƴan cikin gwamnati da ƴan siyasa a matsayinsu na ƴan uwa a gare su sun bar su suna fafutukar ceto ran sarkin su kaďai.

Don haka ne majiyar ta ce suke kira ga gwamnati da ɗaukacin al’umma da su taimaka wajen tara kuďin zuwa miliyan N50 domin ceto ran sarkin wanda a yanzu ya ke cikin haɗari.

Kazalika, ta kuma ce suna kira ga Sanata Dino Melaye, Sanata Sunday Karimi, Hon. Leke Abejide, Hon. Falake, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da sauran ƴan siyasa a jihar da su taimaka wajen ceto sarkin.

Haka kuma suna kira ga fastoci da malamai da su sanya su acikin adu’o’insu domin samun mafita game da lamarin.

By Babaji