EFCC da ICPC: Majalisar Dattawa na yunƙurin kafa hukumar ƙwato kaddarori

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A ranar Talata ne ƙudirin dokar da ke neman yin gyara ga dokar da ta shafi laifuka na shekarar 2022 ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Dokokin ƙasa, tare da ba da shawarar kafa wata sabuwar hukuma da za ta kula da ƙwato kadarori daga haramtattun ayyuka.

ƙudirin, wanda Sanata Idiat Oluranti Adebule (Legas ta Yamma) ta ɗauki nauyinsa, ana kiran sa da ‘Bill Proceeds of Crime (Recoɓery and Management) Bill, 2025 (SB. 343)’.

Ta yi nuni da cewa, ƙudirin na nufin inganta daidaito, gaskiya, da inganci wajen karɓe ƙwato kadarori daga hukumomi 18 da ke da alhakin hakan.

Da yake jagorantar muhawarar da aka yi a zauren majalisar dattawa, Sanata Adebule ya bayyana gyaran a matsayin matakin da ya dace don magance ayyuka da suka kunno kai da gazawar da ke tattare da wannan doka.

Ta ƙara da cewa, tsarin da ake da shi, wanda ya ba da alhakin bincike, shari’a, da gudanarwa ga hukumomi irin su EFCC, ICPC, da Hukumar Kwastam ta Nijeriya, ya haifar da rashin daidaituwa da kuma batutuwan rashin gaskiya.

Adebule ya ce, “Tsarin da ake yi a halin yanzu yana hana ƙasar samun cikakkiyar fa’idar ƙwato kadarori, yayin da ƙungiyoyin da suka dace ke gudanar da ayyukansu ba tare da wani tsarin aiki ba,” inji Adebule.

Ta yi bayanin cewa a ƙarƙashin dokar ta 2022, kowanne daga cikin hukumomi 18 da aka zayyana sun kafa nasu Hukumar Kula da Laifuka, wanda ya haifar da ruɓanya ayyuka, rashin haɗin kai, da kuma rashin isassun kariya ga kadarorin da aka ƙwato.

A cewarta, gyaran da ake shirin yi na neman, “kafa hukuma guda ɗaya tilo mai zaman kanta wacce ke da alhakin gudanarwa da tafiyar da kadarorin da aka ƙwato.

Sanata Adebule ya jaddada cewa, akwai irin wannan nau’in a wasu ƙasashe irin su Birtaniya da Amurka da Ostireliya da kuma Afirka ta Kudu, inda alhakin gabatar da ƙara da sarrafa kadarorin ya bambanta.

By ukarofi