Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) na Arewa maso Yamma, kuma ɗan jam’iyyar adawa, Salihu Lukman, ya musanta rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai ke yaɗawa na cewa shugabannin jam’iyyar adawa sun amince da jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, a matsayin jam’iyyar da za ta tsaya takara a zaɓen 2027 mai zuwa.
Mista Lukman, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana rahoton da kafafen yaɗa labarai suka yaɗa a matsayin ƙarya da yaudara.
Ya kuma yi zargin cewa an dasa labarin ne a kafafen yaɗa labarai domin haifar da rashin jituwa a tsakanin shugabannin ‘yan adawa da ke zawarcin ƙawancen.
Shi ma tsohon Darakta Janar na ƙungiyar gwamnonin ya musanta iƙirarin da wata kafar yaɗa labarai ta intanet ta yi cewa an naɗa shi shugabancin sakatariyar jam’iyyar.
Yayin da yake jaddada cewa tattaunawar ta kai ga matakin da ya dace, ya ce za a sanar da jama’a sakamakon da ya dace a lokacin da ya dace.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Ya kamata jama’a su yi watsi da labarin domin gaba ɗaya ƙarya ne, babu wani hukunci da aka yanke, haka nan kuma ƙarya ce rahoton cewa gamayyar jam’iyyar ta ADC a taronta a ranar Talata, 20 ga watan Mayu, 2025.
“Gaskiyar magana ita ce, ana samun ci gaba sosai a tattaunawar da ake yi a tsakanin shugabannin gamayyar jam’iyyu, kuma nan ba da jimawa ba za a yanke hukunci na ƙarshe game da tsarin siyasar zaɓen 2027.
“Abin takaicin shi ne, da alama akwai wasu ɓata-gari da suke yaɗa labarai a kafafen yaɗa labarai da nufin haifar da rashin jituwa a tsakanin shugabannin gamayyar jam’iyyun.
“Ya kamata jama’a da kafafen yaɗa labarai su yi watsi da duk waɗannan munanan labarai.”
