Gwamnatin Edo na asarar dala biliyan ɗaya wajen yaƙi da rikicin ƙungiyoyin asiri – Gwamna Okpebholo

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya bayyana cewa jihar na asarar sama da dala biliyan ɗaya da za a iya amfani da a wajen waka hannun jari a duk shekara sakamakon mummunan tasirin ƙungiyar asiri da tashe-tashen hankula masu nasaba da ƙungiyar asiri a jihar. 

Okpebholo, wanda ya bayyana hakan a Benin a ranar Laraba, ya ce ba wai kawai munanan asarar rayuka da dukiyoyi ƙungiyoyin asiri ke yi lba, har ma da hana saka hannun jari da yawon buɗe ido, tare da daƙile ci gaban tattalin arziki a jihar.

Ya yi nuni da cewa, yawaitar tashe-tashen hankula masu nasaba da ƙungiyoyin asiri a cikin shekaru biyar da suka gabata ya haifar da cikas ga harkokin tattalin arziki, yayin da masu zuba jari da ‘yan kasuwa ke ƙara yin kaffa-kaffa game da matsalar tsaro.

By ukarofi