Bayan shekaru tara, DSS ta biya diyyar harbin ɗan kasuwa bisa kure a Jos

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ƙoƙarinta na cika alķawarin bada magani kyauta ga basakkwacen ɗan kasuwa da aka harba bisa kuskure shekaru tara da suka gabata yayin atisayen jami’an DSS, hukumar ta gayyaci mutumin zuwa asibitinta dake Abuja.

A tsakiyar watan Maris ne Darakta-Janar na DSS, Tosin Ajayi ya amince da biyan Naira miliyan 10 a matsayin kuɗin dameji ga ɗan kasuwar bisa umarnin wata kotu shekaru shida da suka gabata.

Haka kuma daraktan ya ƙara wa mutumin miliyan N10 na jinkiri da aka samu, wanda ya mayar da jimillar kuɗin zuwa miliyan N20.

Ya kuma umarci asibitin da ta sanya ɗan kasuwar zama ɗaya daga cikin masu amfana da kula da lafiyarsu a kyauta ta yadda zai riƙa samun kulawa ba tare da biyan kuɗi ba a duk lokacin da ya ke son a duba lafiyarsa a asibitin.

Wata majiya daga DSS ta ce, an sanya mutumin a sashen mutane na musamman a asibitin bisa umarnin daraktan, inda hatta abinci kawo masa ake yi yi a ƙarƙashin umarnin DG’n.

A shekarar 2016 ne a yayin atisayen kamo wani mai haramtaccen safarar bindigu a Jos, Jihar Filato, jami’an hukumar suka yi harbin da ya yi sanadin raunata ɗan kasuwar, wanda takwara ne ta fuskar suna da wanda ake zargin.

Daga bisani an kama wanda ake zargin, sannan a 2018 wata kotu a Bauchi ta umarci DSS da ta biyan miliyan N10 ga ɗan kasuwar.

By Babaji