Tsaro: Gwamnatin Katsina ta kashe Naira biliyan biyar wajen samar da kyamarori masu hangen nesa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ya faɗi haka a hirar musayar ra’ayi da aka gudanar a taron “Arewa Tech Test” watau taron gwada fasaha da ƙirƙire ƙirƙire a Arewa.

Ya ce amfani da fasaha shine mafita wajen shawo kan matsalolin tsaro a yankunan da suke fama da rashin tsaro.

Haka kuma Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatin sa na shirin amfani da fasaha wajan sauya akalar ci gaban jihar,tare da nufin mayar da Katsina cibiyar ƙirƙire ƙirƙire da fasahar zamani ta Arewacin Najeriya nan da shekara 2030.

Gwamnan ya bayyana taron da ya gudana na da nufin jawo hankalin masu zuba jari da haɗin gwiwar masu ƙirƙira domin gina makomar matasa a fannin fasaha ,

Ya ce tunda zuwan su mulki muka gudanar da binciken asali a ɓangarori daban-daban da suka haɗa da kiwon lafiya,noma da ilmi.”Domin haka bayanai sahihai suna taimakawa wajen tsara aiki da raba albarkatu yadda ya kamata”inji Dikko Raɗɗa.

Gwamnan ya kuma bayyana kafa hukumar ƙididdiga ta Jihar Katsina wadda ke gudanar da bincike kan matsalar talauci a faɗin jihar.

Ya ce yanzu haka an ƙaddamar da tsarin e_health a manyan asibitocin jihar domin tabbatar da cewa bayanan marasa lafiya suna samuwa a duk inda aka tafi.

“Muna son Katsina ta zama jagora Wajen fasaha da ƙirƙire ƙirƙire a Arewa. Da yardar Allah,nan da shekarar 2030 zamu zama abin koyi wajen ƙirƙira da fasahar zamani “gwamnan ya ce.

Gwamnan ya bayyana ƙwarin gwiwan sa kan makomar jihar,”muna ƙoƙarin mu gina tsarin da zai canza yadda muke aiki, yadda muke tunani da ɗabi’unmu” ya ce.

Taron Arewa Tech Fest wanda ya gudana a Katsina tare da goyon bayan gwamnatin jihar,na da nufin bunƙasa fasaha a yankin Arewa da jawo hankalin masu zuba jari da masu ƙirƙire ƙirƙire daga sassa daban-daban.

By ukarofi