Gwamnatin Amurka ta haramta ɗaukar ƴan Nijeriya da wasu ƙasashe a Jami’ar Harvard

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwmanatin Amurka ƙarƙashin jagorancin Shugaba Donald Trump ta dakatar da daukar ƴaƴan Nijeriya da na wasu ƙasashe a Jami’ar Harvard.

A ranar Alhamis ne Ofishin harkokin tsaro na cikin gida ya ce an janye bai wa daliban ƙasashen waje guraben karatu a Jami’ar.

Haka kuma daliban da suke karatu an ba su zaɓin neman barin makarantar ko kuma a tilasta musu ficewa.

Rahotanni sun bayyana cewa, jami’ar ta gaza cika ķa’idar samar da kuɗi na gwamnatin Trump a sakamakon ƙin bada haďin-kai ga buƙatun Shugaban ƙasar.

Daga cikin ababen da jami’ar ta ƙi yi akwai rashin kawo ƙarshen nuna wariya ga banbance-banbance, daidaito da shirye-shiryen damawa da ɓangarori mabanbanta.

Saidai, Jami’ar ta ayyana hukuncin a matsayin abinda aka yi ba bisa doka ba, inda ta ce ta duƙufa wajen cigaba da kare tsarinta na ɗaukar dalibai daga sama da ƙasashe 140 a faɗin Duniya, kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa.

A zangon karatu na 2024/2025, ďaliban ƙasashen waje, waɗanda suna wakilta kaso 27.2 na ďaliban makarantar, sun shiga halin tsaka-mai-wuya game da matsayin bizarsu da karatukansu gami da damanmakinsu na rayuwa.

By Babaji