Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa ‘yan Majalisar Dokoki ta ƙasa ba an zaɓe su ba ne domin su yi taƙaddama da ɓangaren zartarwa na gwamnati, sai dai don su inganta manufofin da ke ƙara ci gaban ƙasa.
Shugaban Majalisar Dattawan ya yi wannan bayani ne a wani taron ƙaddamar da wani fim da za a saki domin bikin cika shekaru biyu da mulkin Bola Tinubu.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata, Akpabio ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin ɓangaren majalisa da na zartarwa, inda ya ce: “Lokacin da aka zaɓe ka zuwa Majalisar Dokoki, ko dai a Majalisar Dattawa ko Wakilai, al’ummarka ba za su ba ka safar dambe ba. Ba gasa ce ta dambe ba. An tura ka ne domin ka yi aiki cikin haɗin kai don amfanin Nijeriya.”
Shugaban Majalisar Dattawan ya jaddada cewa dangantaka tsakanin ɓangarorin gwamnati biyu ta kasance cikin kwanciyar hankali a cikin shekaru biyu da suka wuce, saboda hangen nesa na ci gaban ƙasa.
“Idan ka bata duka ƙarfinka wajen yaƙar ɓangaren zartarwa, wa zai yi aikin ci gaban Nijeriya?” in ji shi. Ya ƙara da cewa wannan gwamnatin ta bambanta a tarihin Nijeriya, domin shugaban ƙasa, uwargidansa, da mataimakin shugaban ƙasa duk tsofaffin ‘yan majalisa ne.
