Gwamnatin Zamfara ta ƙaryata labarin gurfanar da wata matashiya bisa zargin yin ridda

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya ƙaryata wani rahoto da wata jarida ta intanet ta buga na cewa wata ‘yar asalin jihar mai suna Zainab Muhammad na fuskantar shari’a a kotun shari’ar Musulunci bisa zargin ta da fita daga addinin Musulunci zuwa Kiristanci.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Idris ya fitar, gwamnan ya bayyana rahoton a matsayin na ƙarya, inda ya zargi waɗanda suka rubuta rahoton da nufin tayar da rikicin addini a jihar.

Idris ya bayyana cewa Grand Khadi na jihar ya tabbatar da cewa babu wani labari na irin wannan shari’a a cikin kotunan shari’ar musulunci a jihar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa: “Hankalin gwamnatin jihar Zamfara ya karkata ga wani mummnan labari na ƙarya da ke yawo kan wata ‘yar shekara 22 mai suna Miss Zainab Muhamadu, wai cewa ta na fuskantar hukuncin kisa saboda ta koma Kiristanci.

“Muna so mu bayyana cewa aikin maƙiya zaman lafiya ne, waɗanda suke kan gaba wajen haifar da tashin hankali inda babu.

“Labarin ƙaryar, wanda wata jarida ta yanar gizo ya yi kaurin suna wajen yada labaran da ba a tabbatar da su ba da aarya, ba wani abu ba ne illa yunƙurin dagula zaman lafiya, kuma mun gode Allah buƙatarsu ba ta biya ba.”

By ukarofi