‘Yan sanda sun ceto mutum 28 da aka yi garkuwa da su tare da kama mutum 10 a ƙasar nan

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta bayyana cewa ta ceto mutum 28 da aka yi garkuwa da su sannan ta kawo wasu maza 10 wanda take zargin masu garkuwa da mutane a kasar nan.

Daniel Ndukwe kakakin rundunar ya sanar da haka a wani takarda da manema labarai suka samu ranar Talata a garin Enugu.

Ndukwe ya ce makamai da suka hada da bindigogi da harsasai, kudi, motoci da dai sauran haramtattaun kaya na daga cikin kayan da jami’an tsaron suka kwato.

Yadda Jami’an tsaron suka ceto mutanen da aka yi garkuwa da su tare da kamo masu garkuwa da mutane.

Ndukwe ya ce jami’an rundunar dake aiki a karkashin rundunar yaki da garkuwa da mutane sun ceto mutum daya ranar 13 ga Mayu da karfe 9:45 na dare a hanyar Enugu zuwa Fatakwal a jihar.

Ya ce jami’an tsaron sun kwato motoci da suka hada da Toyota Camry na mutumin da aka yi garkuwa da shi, Toyota Corolla da maharan suke amfani da shi, da Leɗus 330SUɓ duk a hanyar Premier Layout, Independence Layout a jihar.

Kakakin ya ce rundunar na farautar masu garkuwa da mutane domin ganin ta kamo su Kuma an yanke musu hukunci.

Ndukwe ya ce da misalin karfe biyar da rabi na daren ranar 14 ga Mayu ‘yan sandan dake Igbo-Eze ta Arewa tare da hadin gwiwar sojojin da ‘yan banga sun ceto .utim 21 da aka yi garkuwa da su a kauyen Amaka-Okpodu dake jihar Kogi.

“Maharan sun yi garkuwa da wadannan mutane yayin da suke hanyarsu ta dawowa daga daurin aure a hanyar Iyionu zuwa Aguibeje dake karamar hukumar Igbo-Eze ta Arewa ranar 10 ga Mayu.

“Jami’an tsaron bayan sun tattaro bayanan sirri sun kuma kama wasu maza biyar da suke zargin suna da hannu a garkuwa da mutane. Sun Kuma kwato bindigogi uku daga hannun maharan.

Kakakin rundunar ya ce motsa kirar mini bus da babura hudu duk na mutanen da aka yi garkuwa da su na daga cikin ababen da jami’an tsaron suka kwato.

Ya ce a ranar Lahadin da ya gabata ‘yan sandan dake aiki a Umumba tare da hadin ‘yan banga, mafarauta da mutane sun ceto wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su.

Ndukwe ya ce an yi garkuwa da wadanda mutane inda a cikin su akwai maza biyu da mata biyu a hanyar Umumba zuwa Ndiuno zuwa Aguoba dake karamar hukumar Ezeagu.

“Jami’an tsaron sun samu nasarar kama wasu maza hudu da ake zargin suna da hannu a yin garkuwa da wadannan mutane.

Ndukwe ya ce da karfe 6:34 na yamma ‘yan sandan dake aiki a Ninth Mile sun ceto tare da kama wani da ake zargin yana garkuwa da mutane daga hannun mutane yayin da suke lakada masa daukan tsiya.

“Jami’an tsaron sun samu labarin cewa wannan mutum tare da wasu mutane uku sun yi kokarin yin garkuwa da wata mata inda bayan ta yi ihu ne mutane suka kawo dauki inda a cikin su uku suka gudu sannan aka kama daya daya cikinsu.

“Jami’an tsaron sun kai mutum daya din da mutane suka lakadawa daukan tsiya amma yana tsare a ofishinsu yana kuma taimakawa jami’an tsaron da bayanan da za su taimaka wajen kamo sauran masu garkuwa da mutanen da suke aiki tare.

Ya ce a ranar Asabar ɗin da ta gabata ‘yan sandan dake aiki a Okpuje tare da hadin gwiwar ‘yan banga da mafarauta sun gano wasu mutane biyu dauke da naira 70,000, 150,000, buredi da lemun kwalba a dajin Okpuje dake tsakanin jihar Enugu da Odolu jihar Kogi.

“Jami’an tsaron sun hadu da wadannan mutane da suke hanyar su na kai wadannan kaya wa maharan da suka yi garkuwa da ‘yan uwan su dake boye a dajin.

“Maharan sun gudu da raunin harsashi a jikinsu bayan sun yi bata kashi da jami’an tsaron.

“Jami’an tsaron sun ceto mutanen dake tsare a hannun maharan sannan sun kwato bindiga kirar pump action daya, harsasai da wasu haramtattaun kaya daga dajin.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bitrus Giwa bayan ya mika godiyarsa ga kokarin da jami’an tsaron suka yi ya tabbatar cewa ba za su yi Kasa da gwiwar ba wajen ganin sun samar da tsaro a jihar.

Giwa ya yi kira ga mutane da su zama masu kiyaye doka da oda tare da mara wa jami’an tsaro baya domin samar da tsaro a jihar.

By ukarofi