
Daga BELLO A. BABAJI
A daren ranar Alhamis ne jami’an Sojojin Nijeriya a ƙarƙashin atisayen HAƊIN KAI suka kare wani hari da mayaƙan Boko Haram suka kai a sansanin sojoji dake Ƙauyen Gajibo na Ƙaramar Hukumar Dikwa a Jihar Borno.
Mataimakin Daraktan hulďa da jama’a na sojoji shiyya ta 7, Ajemasu Yake Jingina ya bayyana hakan a wata takarda, ranar Juma’a, inda ya ce mayaƙan Boko Haram na ɓangaren Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad (JAS) da ISWAP ne suka kai farmakin da misalin ƙarfe 10:20 na dare.
Lamarin da ya ankarar da dakarun sojojin tare da mayar da martani cikin gaggawa da ɗauki daga Hedikwatar Birget da Bataliya ta 134 ta jami’ai na musamman.
A nan ne aka kashe ƴan ta’adda biyar tare da ƙwato wasu muggan makamai masu yawa.
Ya bayyana cewa, daga cikinsu akwai bindigar AK101 da mazubin alburusai da ke ɗauke da alburusan 5.56mm NATO guda 13 da kuma na 7.62mm guda 51.
Sauran sun haɗa da ababen fashewa na gurnet, safar fuska guda biyu, rediyon Baofeng, fitilar hannu da takalmin ‘desert boots’.
Ya ƙara da cewa, dakarun sojoji duk da ķalubalen da suke fuskanta suna cigaba da ƙoƙarin daƙile ayyukan ta’addanci a shiyyar Arewa maso Gabas da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.
