
Daga BELLO A. BABAJI
Mutane 20 ne aka kama bisa laifin yin kutse ga na’urar jarrabawar UTME ta shekarar 2025 da Hukumar JAMB ta shirya.
Jami’an DSS da na ƴan sanda ne suka kama waɗanda ake zargin a Abuja.
Ana zargin mutanen suna daga cikin wata ƙungiya da ke da sama da mambobi 100, waɗanda suka ƙware wajen yin kutse ga shafukan jarrabawa da dama da suka haɗa da JAMB da NECO.
Majiya daga jami’an tsaro sun ce, waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu da cewa suna da hannu a yin kutse ga ofishin sadarwar CBT domin ɗora wa JAMB laifi da karya kwarin-gwiwar ďaliban da za su yi NECO da WAEC a komfuta nan gaba.
Haka kuma, sun yi kutsen ne da nufin bada maki mai yawa ga ďaliban da suka biya cin hancin kuɗaɗe tsakanin N700,000 da miliyan N2.
An ruwaito cewa, mambobin tawagar da dama suna da makarantun kuɗi da kwaleji-kwaleji da tara maƙudan kuɗaɗe a cibiyoyinsu na musamman.
Wani sharhi da aka yi ya nuna cewa, sama da kaso 78 na ďaliban sun samu ƙasa da maki 200 cikin 400 na jarrabawar.
A ranar 14 ga watan Mayu ne Rajistiran hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ya ce sakamakon dalibai guda 379,997 a cibiyoyi 157 ne suka samu tsaiko a yankunan Legas da Kudu masu Gabas.
