Kwamitin Amitattun MOPPAN ya je ta’aziyyar rasuwar shugaban ƙungiyar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Asabar ne mambobin kwamitin amitattu na ƙungiyar masu shirya fina-finai (MOPPAN) suka je Zaria domin gabatar da ta’aziyyar rasuwar shugaban ƙungiyar, Alhaji Umar Maikuďi.

Tsohon shugaban ƙungiyar, wanda ya samu wakilcin Dakta Ahmad Sarari shi ya gabatar da addu’a a madadin mambobin kwamitin.

Kwamitin ya kuma miƙa ta’aziyyar ƙungiyar ga iyalan mamacin bisa babban rashin da aka yi musu tare da fatan samun haƙurin juriyan rashin a gare su.

By Babaji