Daga USMAN KAROFI
Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC Ltd) ya sanar da cewa za a rufe matatar mai ta Fatwakal daga ranar 24 ga Mayu, 2025, domin gudanar da gyare-gyare da duba lafiyar ayyukanta. Wannan rufewa, a cewar sanarwar da mai magana da yawun kamfanin, Femi Soneye ya fitar, na daga cikin shirye-shiryen kiyaye ingancin aiki da ɗorewar masana’antar man fetur a Najeriya.
Sanarwar ta bayyana cewa NNPC na aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomi masu ruwa da tsaki, ciki har da hukumar kula da harkokin iskar gas da man fetur a matakin tsaka da na ƙasa (NMDPRA), domin tabbatar da cewa aikin gyaran zai gudana cikin inganci da gaskiya. NNPC ta kuma jaddada ƙudirin ta na ci gaba da samar da wutar lantarki da makamashi mai ɗorewa ga ‘yan ƙasa.
Wannan ba shi ne karon farko da aka rufe matatar ba, domin a watan Disamba na shekarar 2024 ma an dakatar da ayyukan matatar bayan dawowa daga gyaran da ya laƙume dala biliyan 1.5. Kamfanin ya sha alwashin ci gaba da sabunta bayani ga jama’a ta kafafen sadarwa a hukumance yayin da gyaran ke gudana.
