Jami’ar Harvard ta maka Trump a kotu bisa hana ta ɗaukar ƴan ƙasashen waje

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a ne Jami’ar Harvard dake Amurka ta shigar da Gwamnatin Shugaba Donald Trump ƙara a kotu, bisa hana ta ɗaukar ďalibai ƴan ƙasashen waje.

A ranar Alhamis ne Sakataren harkokin tsaro na cikin gida a Amurka, Kristi Noem ya sanar da haramta wa Jami’ar ɗaukar ďaliban, lamarin da ya jefa dubunnansu shiga mawuyacin hali.

Shugaba Trump ya fusata ne da Jami’ar a lokacin da ta yi buris da buƙatarsa game da sauya tsarinta na ɗaukar dalibai karatu da bada ayyukan wucin-gadi.

Gwamnatin ta kuma yi barazanar ƙaƙaba wa Jami’ar biyan Dala biliyan 9 na kuɗin haraji da wasu sharuďďa masu tsauri.

Soke karatu ga ďaliban ƙasashen waje a jami’ar zai sa ta yi asarar maƙudan kuɗaɗe duba da cewa sune ke wakiltar kaso ɗaya bisa huɗu na adadin ďalibanta.

Jami’ar, a wata takarda ta hannun shugabanta, Alan Garber, ta yi alla-wadai da hukuncin inda ta kira hakan da abinda aka yi ba bisa doka ba.

By Babaji