
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar masu shirya fina-finai ta Arewa (AFMAN) reshen jihar Kano, ta miƙa ta’aziyyarta ga rasuwar Shugaban ƙungiyar masu shirya fina-finai ta ƙasa (MOPPAN), Alhamis Umar Maikuďi.
Ta jajenwa iyalai, ƴan uwa da abokan arziƙi bisa babban rashin jajirtaccen jagoran, wanda ya bada gagarumar gudumawa ga masana’antar Kannywood da harkar fim a Nijeriya.
A sanarwar da ke ɗauke da sanya hannun Sakataren AFMAN, Sharif Mustapha Anwar, ƙungiyar ta kuma yi addu’ar fatan samun rahama a gare shi da ɗaukacin al’umma baki ɗaya.

