Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa na jihar Katsina ya tabbatar wa al’ummar jihar Katsina cewa zai ɗauki wasu matakai na bai ɗaya don kawo ƙarshen ta’adanci a jihar.
Dikko ya faɗi haka ne a wata ziyarar ta’aziya a ƙauyen Gobirawa da ke ƙaramar hukumar Dutsinma,biyo bayan mummunar harin ‘yan bindiga da a ka kai ƙauyen da yai sanadiyar mutuwar da dama.
Gwamnan sai ya umurce shugaban ƙaramar hukumar da ya bada sunayen mutane biyar daga cikin al’ummar yankin damin wani muhimmin tattauna yadda gwamnati za ta tallafawa shirye shiryen tsaro na gida.
Yace bayan jin rahoton jami’an tsaro game da shirin kai harin, gwamnati ta tattara jami’an tsaro zuwa ƙauyen”amma abin takaici bayan da jami’an tsaron sun tashi ‘yan bindigan suka kai wa ƙauyen hari.
Malam Dikko Raɗɗa ya kuma buƙaci al’ummar yankin da su cigaba da sa ido da bayyanar da mutanen da ake zargi da haɗin gwiwa da yan bindiga,yana mai jaddada muhimmiyar ruwa da al’umma ke takawa wajen tabbatar da tsaro.
Harin da ‘yan bindigan suka kai a ƙauyen Gobirawa yayi sanadiyar mutuwar mutane 13 da jikkata da dama tare da sawa gidaje da dama wuta a ƙauyen.
Yan kwanakin nan ‘yan bindigan sun zagaya hare hare wasu ƙauyukan da suke ƙananan hukumomin Dutsinma, Safana da ƙanƙara.
