APC a Zamfara ta yaba wa Tinubu kan bai wa Yazid Ɗanfulani muƙami

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara, ta yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan naɗin Hon. Yazid Shehu Ɗanfulani a matsayin MD/CEO na Hukumar Inshorar Aikin Gona ta Najeriya NAIC.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar na jihar Yusuf Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi.

Jam’iyyar ta bayyana naɗin a matsayin abun alfahari ga al’ummar Jihar Zamfara da kuma ɗaukacin ‘yan Nijeriya.

Jam’iyyar ta godewa shugaban jam’iyyar APC na jihar ƙaramin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle, wanda ƙoƙarinsa ya sanya Jihar Zamfara cikin matsayi mai daraja a ƙasar nan.

“Muna tabbatar muku da cewa wannan naɗin zai zama abin alfahari ga gwamnatin Tinubu.”

“A matsayinsa na gogaggen ma’aikacin banki kuma mai fasaha, ko shakka babu Hon. Yazid Ɗanfulani zai taka muhimmiyar rawa don kawo sauyi mai ma’ana.”

Jam’iyyar ta taya sabon MD/CEO na NAIC murna tare da yin kira gare shi da ya ci gaba da zama jakadan Jihar Zamfara nagari a matsayin sa na sabon shugaban NAIC.

“Naɗin nasa ya kawo farin ciki sosai a tsakanin matasan APC na Jihar Zamfara”.

Jam’iyyar ta kuma bayyana Hon. Yazid a matsayin mutum mai gaskiya da ƙwazo a siyasance.

By ukarofi