‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da mutuwar ɗan ta’addan a wata takardar sanar wa da a ka raba wa manema labarai a Katsina.
DSP Sadiq ya bayyana cewa yan bindiga ƙarƙashin jagorancin Audu Kushin suka kai hare hare a ƙauyukan Unguwar Lado da Ƙauyen karo a ƙaramar hukumar Malumfashi.
Sai dai a cewar sa ƴan bindigan basu sami nasara ba,hakan kuwa ya faru ne bayan da ƴan sanda ƙarƙashin DPO na ƙaramar hukumar Malumfashi su ka kai wa al’ummar ƙauyukan ɗauki bayan da aka kwarmata masu bayanan sirri.
Ya ce ƴan sandan sun sami nasarar kashe jagoran ƴan bindigan Audu kushin da ke zaune a ƙauyen Tsamiyar Maigora, sauran ƴan bindigan sun gudu ɗauke da raunuka da suka samu a lokacin artabu da jami’an tsaron ƴan sanda.
Haka kuma ƴan sanda sun sami kuɓutar da mutane biyar da ƴan bindigan su kayi ƙoƙarin sace su,sai dai suma da aka kuɓutar sun samu raunuka daban-daban da a halin yanzu suna babban asibitin Malumfashi ana basu kulawa.
DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa yanzu haka ƴan sanda na farautar ƴan bindigan da suka tsere.
Kwamishinan ƴan sanda a Jihar Katsina CP Bello Shehu ya jinjina wa jami’an nasa bisa nuna ƙwazo da ƙwarewa wajen tunkarar ta’addanci a jihar.
