Yadda rayuwar Hamdiyya ta shiga garari a Sakkwato

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A lokacin da nake wannan rubutu Hamdiyya Sidi Shariff na can na kwance a Babban Asibitin Bakura da ke Jihar Sakkwato, inda take samun kulawar likitoci, bayan ɓatan dabon da ta yi na tsawon wuni guda ba a san inda take ba. Bayanan da lauyanta Abba Hikima ɗan Jihar Kano ya yi sun bayyana cewa, Hamdiyya ta fita ne daga gida zuwa kasuwa yin cefane a jajiberen ranar shigar su kotu, kan shari’ar da suke yi bisa zargin da ake yi mata na amfani da kalaman harzuƙa jama’a da ɓatanci ga Gwamnan Jihar Sakkwato Ahmad Aliyu, amma tun daga lokacin ba a sake ganin ta ba. Sai misalin ƙarfe goma na dare bayanai daga lauyan nata suka fara fitowa kan cewa an gano ta a wani ƙauye, cikin mawuyacin hali, har ma an garzaya da ita asibiti.

Jama’a da dama na zargin da hannun gwamnatin jihar kan wannan al’amari da ya faru na sace wannan matashiya, wacce kafin haka ta faru babu wanda ya san da ita. Amma fitowar bayanai game da ƙorafin da ta yi akan al’ummar ta, ya sa ta zama fitacciyar, har gwamnatin jiha na shari’a da ita. Kodayake, babu inda ya nuna a zahiri akwai hannun gwamnati a cikin sace wannan yarinya, amma biri ya yi kama da mutum, domin kuwa wannan ba shi ne karon farko da ake kai wa rayuwar ta farmaki ba. Ko a watannin baya ma sai da aka zargi wasu ɓatagarin matasa da ke da alaƙa da gwamnati sun farmaki rayuwarta.

A gaskiya tun a farko ma an yi kuskuren yadda aka tunkari batun yarinyar nan, domin babu inda kalamanta suka bambanta da sauran maganganu da jama’a ke yi a kafafen sada zumunta na ’yancin faɗar albarkacin baki. Amma sai wasu masu fushi da fushin wani suka fassara maganganun nata da siyasa, aka kuma canja wa abin manufa da cewa ta ci mutuncin Gwamna. Ana amfani da kafafen watsa labarai da wuraren tarukan siyasa da na addini ana aibata ta a matsayin marar tarbiyya, da ganin girman mutane.

Zargin da ake yi wa Gwamnatin Jihar Sakkwato, da ’yan bangar siyasarta, na cigaba da ɗaukar hankalin ‘yan Nijeriya, musamman matasa da ƙungiyoyin mata, da masu kare haƙƙoƙin ɗan adam. Yayin da ake cigaba da yin Allah wadai da abin da ake zargin ‘yan koren gwamnati sun yi mata na sacewa da tozarcin da aka yi mata, wanda yanzu haka ya jefa rayuwarta cikin haɗari. Duk da kasancewar an sanya jami’an tsaro a asibitin da ake kula da lafiyarta, amma firgici da tsoron da take ciki, abin damuwa ne matuƙa. Kuma hakan zai iya shafar shari’ar da take fuskanta, wajen fitar da gaskiya, da iya samun natsuwar kare kanta a gaban kotu.

Har kawo yanzu babu cikakkun bayanai game da asalin abin da ya wakana na sace ta da cin zarafin da aka yi mata, sakamakon halin da take ciki a halin yanzu a asibiti. Amma babu shakka idan Allah Ya sa ta farfaɗo sosai, kuma ta samu ƙwarin gwiwar yin magana, ba tare da tsoro ba, jama’a za su san gaskiyar me ya faru, ko su waye suka yi mata abin da suka yi mata.

Idan za a iya tunawa, wannan yarinya Hamdiyya Sidi Sharif ta yi wani bidiyo ne da ya yaɗu sosai a zaurukan sada zumunta, inda take zargin Gwamnatin Jihar Sakkwato da jami’an tsaro da gaza ɗaukar mataki kan halin da ake ciki na taɓarɓarewar tsaro a jihar. A maimakon a yaba mata a matsayinta na matashiyar mace da ta nuna damuwa da kulawa kan halin da mata da yaransu a ƙauyukan jihar ke ciki, da kuma yadda rayuwar waɗanda ke zaman gudun hijira a cikin garin Sakkwato ta shiga wani yanayi marar daɗi, sai ‘yan koren gwamnati da muƙarrabanta, har da wasu malaman addini, suka riƙa sukar maganganunta ana juya batun da sunan ta yi wa Gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu, rashin kunya.

A maimakon a dubi saƙon da take isarwa, don gwamnati ta ƙara ƙaimi kan ƙoƙarin da take cewa tana yi a harkar tsaro, har ma ƙila a yaba wa gudunmawar da jama’ar jihar ke bayarwa na shawarwari da bayanan sirri, sai aka nemi mayar da abin siyasa, har da jefa rayuwar Hamdiyya cikin mugun yanayi, da ake neman ɗaukar ranta. Bayan tsare ta da ‘yan sanda suka yi na wani lokaci, don tsorata ta da rufe mata baki. Wannan abin da suka yi kuma shi ya ƙara fitar da batun da ake yi na tauye wa jama’a ‘yancinsu na faɗin albarkacin baki, a yanayin da ake ciki na lalacewar tsaro. Sannan matakan da ake ɗauka akan yarinyar ya ƙara sa ta zama marar tsoro kuma sunanta ya ƙara fita a duniya, a matsayin wacce ake zalunta, don ta yi magana a yanar gizo! A yayin da wasu ‘yam mata da, samari ke can a tiktok da Facebook suna rawar baɗala da maganganun batsa, suna zubarwa kansu mutunci da iyayensu.

Manufar rubutuna ba duba ko abubuwan da ta yi zargi a kansu haka ne ko ba haka ba ne, amma dai ina so ne mu duba ƙalubalen da ake samu game da yadda matasa ke amfani da zaurukan sada zumunta, da kuma tasirin su. Ba kamar a baya ba, a yanzu jami’an tsaro suna sa ido sosai ga abubuwan da jama’a ke rubutawa su yaɗa a shafukansu na manhajojin sada zumunta.

Idan za mu iya tunawa tun a shekarar 2019 da Majalisar ƙasa ta amince da kafa dokar da za ta yi yaƙi da yaɗa labaran ƙarya da bayanan da za su iya zama haɗari ga al’umma, ake ta samun ƙorafe-ƙorafe daga ‘yan Nijeriya da ƙungiyoyin ƙare ’yancin ɗan adam, game da tanade-tanaden dokar da yadda za a iya amfani da ita a murƙushe mutane masu bayyana ra’ayoyinsu. Kamar dai yadda muke iya gani yanzu. Kodayake ba ina nufin kafa doka don yi wa mutane dabaibayi ko linzami game ayyukansu da abubuwan da suke yaɗawa kuskure ba ne, lallai akwai buƙatar sa ido sosai, don inganta tsaro da zaman lafiya da kiyaye haƙƙoƙin jama’a, matuƙar za a kiyaye da haƙƙoƙin ɗan adam. Amma kafa doka don a takurawa mutane da hana su sakewa ko faɗar gaskiya bai dace ba.

Sannan kuskure ne jami’an tsaro su bari ‘yan siyasa na amfani da su wajen farmakar waɗanda ake kallo a matsayin ‘yan adawa, ko masu ƙalubalantar manufofin gwamnati. Har yanzu ba mu manta da ɓacewar matashin nan ɗan Kaduna da ake kira Abubakar Idris Dadiyata ba, wanda har kawo yanzu da nake wannan rubutun ba a san a inda yake ba. An zargi jami’an tsaro da ɗauke shi su kai shi wani ɓoyayyen waje, don rufe masa baki kan irin rubuce-rubucen da yake yi, da a ciki yake yawan sukar wasu tsare-tsare da manufofin gwamnati. Tun a ranar 1 ga watan Agusta na shekarar 2019, da aka tafi da Dadiyata, har kawo yanzu babu shi babu labarinsa.

Labarin Hamdiyya da Dadiyata ya kusa zuwa ɗaya, kodayake ita har kawo yanzu ana iya ganin ta a raye, tana shaƙar iskar ’yanci. Ba kamar fargabar da jama’a suka fara nunawa, lokacin da aka shiga zullumin ɓacewarta ba. Alhalin shi kuwa Dadiyata babu ma tabbas ɗin ko yana raye. Rahotanni da dama na ƙara nuna fargaba da tsoro kan zarge-zarge da ake yi cewa akwai wasu jami’an tsaron da ake amfani da su wajen murƙushe masu sukar gwamnati ko ‘yan siyasa, ta hanyar tsorata su ko yi musu wata barazana.

Amfani da ƙarfin hukuma ko bakin bindiga ko ‘yan bangar siyasa, a toshe bakin mai faɗar ra’ayinsa kan wata magana ko wani al’amari da yake faruwa a jiharsa, yana zubar da kimar gwamnati da jami’anta. Ana ganin hakan a matsayin nuna son zuciya ko tauye haƙƙin faɗin albarkacin baki, wanda ya saɓawa, dokokin ƙasa da tanadin Majalisar ɗinki Duniya. Yana da kyau a riƙa nazari da bin wasu hanyoyi na ƙaryata maganganun da ba na gaskiya ba, ko fayyace zarge-zargen da ake yi wa gwamnati, wanda ita take tunanin ba a yi mata adalci ba.

Duk da zargin tauye haƙƙin da ake yi wa gwamnati da jami’an tsaro kan masu sukar gwamnati, dole ne kuma a yaba musu ta wani ɓangaren saboda yadda suke ƙoƙarin daƙile masu amfani da zaurukan sada don hassala rikici ko tashin hankali. Kamar yadda aka yi ram da wani matashi mai suna Suleiman Yakubu da ya yi wa kansa bidiyo yana kira ga matasa su ɗauki doka a hannu wajen yin fashe-fashe da ƙone-ƙone a cikin garin Jos, a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a wasu sassan ƙasar nan a shekarar da ta gabata. Kun ga wannan abu ne da ya dace, domin daƙile ɓarna da inganta tsaro.

A yayin da nake jan hankalin hukumomi a Jihar Sakkwato da masu faɗa a ji na jihar su tabbatar da tsare ‘yanci da mutuncin wannan baiwar Allah Hamdiyya, da bi mata haƙƙinta na cin zarafin da aka yi mata, ina kuma kira ga matasa su guji amfani da zaurukan sada zumunta ta hanyoyin da ba su dace ba. A kaucewa cin mutuncin manya ko aibata su, a nisanci yaɗa jita-jita da labaran ƙanzon kurege, ko jirkita bayanan gaskiya, da nufin cimma wata manufa ta siyasa ko son zuciya. Lallai mu sani yanzu fa ba da ba ne, akwai dokoki masu tsauri a ƙasar nan game da masu amfani da zaurukan sada zumunta suna yin abubuwan da basu kamata ba. In kunne ya ji an ce gangar jiki ta tsira.

By ukarofi