Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta musanta iƙirarin cewa, an ƙaddamar da wani kwamiti da zai mayar da malaman da ake ɗaukar nauyin ƙarin karatunsu a ƙasashen waje (BEA) zuwa jami’o’in Nijeriya, inda ta bayyana labarin a matsayin ƙarya da yaudara.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta fitar ta hannun daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Boriowo Folasade a ranar Asabar, 17 ga Mayu, 2025.
Gwamnati a cikin sanarwar ta dage cewa saɓanin rahotannin da kafafen yaɗa labarai ke yaɗawa, babu wani shiri irin wannan. Don haka, gwamnati ta ce, “An shawarci jama’a da su yi watsi da wannan mummunan labari gaba ɗaya.”
Gwamnati, duk da haka, ta nanata cewa duk malaman BEA za su ci gaba da samun cikakken goyon bayan gwamnati har zuwa kammala shirye-shiryensu na ilimi, ta ƙara da cewa, “Wannan ya haɗa da koyarwa, alawus, da duk wasu haƙƙoƙi da aka amince.”
Sanarwar ta ƙara da cewa: “An jawo hankalin ma’aikatar ilimi ta tarayya kan wata sanarwar ƙarya da yaudara da ke yawo a kafafen yaɗa labarai mai taken “BEA: Ministan Ilimi ya karɓi rahoton kwamitin.”
“Labarin ƙaryar ya yi ikirarin cewa Ministan Ilimi, Dr. Maruf Olatunji Alausa, ya ƙaddamar da kwamitin da zai sa ido kan yadda za a dawo da malaman jami’o’in Nijeriya (BEA) zuwa wuraren aikin su biyo bayan soke shirin na BEA.
“Ma’aikatar ta bayyana ƙarara cewa ba a ƙaddamar da irin wannan kwamiti ba, kuma babu wani shiri na tilasta malaman BEA dawowa, ana shawartar jama’a da su yi watsi da wannan kuskuren baki ɗaya.
“Kamar yadda aka bayyana a fili a cikin sanarwar manema labarai na hukuma mai kwanan wata 07/05/2025, Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin bayar da tallafin karatu na BEA a matsayin wani ɓangare na canjin manufofin dabaru don ba da fifiko da ƙarfafa ilimin manyan makarantu na cikin gida.
“Wannan shawarar ta biyo bayan nazarin manufofin da aka yi, sanin cewa duk kwasa-kwasan da aka yi karatu a ƙasashen waje ta hanyar BEA a halin yanzu ana samun su—kuma galibi suna da inganci—a cikin jami’o’in Nijeriya da kwalejin fasaha.
“Duk da haka, ma’aikatar ta sake nanata cewa duk malaman BEA da ke gudana za su ci gaba da samun cikakken goyon bayan gwamnati har sai an kammala shirye-shiryensu na ilimi.
“An shawarci jama’a da su dogara kawai da ingantattun bayanai daga tashoshin sadarwa na ma’aikatar.”
