Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya sake jaddada cewa ƙasarsa ba za ta amince Ukraine ta shiga ƙungiyar NATO ba, yana mai cewa hakan barazana ce kai tsaye ga tsaron Rasha. Ya kuma buƙaci a daina yunƙurin shigar da ƙasashen da ke kusa da iyakar Rasha cikin ƙungiyar.
Putin ya ƙara da cewa dole ne a soke duk wani takunkumi da aka kakaɓa wa Rasha, tare da kare haƙƙin ‘yan asalin Rasha da ke Ukraine. Duk da cewa kasashen yamma na goyon bayan ‘yancin Ukraine, wata majiya daga ƙungiyar NATO ta ce, “Za mu ci gaba da kare duk wata ƙasa mai neman tsari da yancin kanta.”
Masana harkokin diflomasiyya sun nuna cewa wannan gargaɗin da Putin ya yi na nuna cewa akwai gagarumin cikas ga yunƙurin tsagaita wuta.
