Sabon nau’in Korona ya ɓulla a ƙasashe da dama – WHO

Spread the love

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbatar da ɓullar sabon nau’in cutar Korona mai suna NB.1.8.1 a ƙasashe da dama, ciki har da Amurka. Wannan sabon nau’in na ɗauke da sauye-sauyen da ke iya shafar yadda rigakafi ke aiki.

Sai dai har yanzu babu wata alama da ke nuna cewa nau’in na da tsanani fiye da waɗanda suka gabata. WHO na ci gaba da bibiyar nau’in, tare da bai wa ƙasashe shawarar tsaurara matakan kariya da cigaba da allurar rigakafi.

By ukarofi