Wata girgizar ƙasa mai ƙarfin gaske ta afku a yankin gabashin Myanmar, inda ta lalata gidaje da tituna tare da janyo asarar rayuka. An bayyana cewa mutane da dama sun mutu, yayin da dubban wasu ke buƙatar mafaka da agaji.
ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa sun fara aika kayayyakin taimako, amma suna fuskantar cikas sakamakon matsalolin tsaro da kuma lalacewar hanyoyi.
Ma’aikatar jin kai ta Majalisar ɗinkin Duniya ta bayyana cewa “lokaci na tafiya, kuma mutane na buƙatar agaji cikin gaggawa.”
