
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno, ya bada tallafin Naira miliyan 5 ga kowane ɗaya daga cikin iyalan jami’an sa-kai na haɗaka, wato CJTF guda takwas da suka rasa rayukansu a yayin fashewar bom a hanyar Dikwa zuwa Marte dake jihar.
Zulum ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, a yayin ziyarar ta’aziyya ga iyalan mamatan a Maiduguri, inda ya kuma yi alķawarin cewa gwamnatinsa za ta ɗauki nauyin karatun ƴaƴansu.
Ga waɗanda ba su da ƴaƴa kuwa, Gwamnan ya ce za su riƙa agaza wa makusantansu ta hanyoyin da suka dace.
Ya kuma ce, hakan wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatinsa wajen tallafa wa iyalan jami’an tsaro na CJTF da suka sadaukar da kawunansu wajen bai wa al’ummarsu kariya.
Kazalika, Zulum ya yi addu’ar fatan samun rahama ga mamatan gami da haƙurin juriya ga iyalan nasu.
A ranar Talata ne jami’an suka rasu, a lokacin da suka bi ta kan wani bom da aka dasa a yankin da suke sintiri.
