Cikar Shekara 2: Matar Gwamnan Zamfara ta bai wa mata 1,018 jari

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta baiwa mata 1018 tallafin jari domin samun damar fara cigaba da sana’o’in da suke da su a wani ɓangare na cika shekaru biyu da mijinta ya hau kan karagar mulki.

An zaɓo mata 1,018 ne daga ƙananan hukumomi 14 na jihar.

Waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun samu tallafin kayan fara sana’o’insu da suka kunshi Wajen Suya, Farin Wake, Zoborodo, Dankali da Man Girki tareda basu Naira 20,000 kowannensu.

Hajiya Huriyya ta yi nuni da cewa, an tsara wannan tallafin ne domin bayar da tallafi ga matan da ke gudanar da ƙananan sana’o’i daban-daban.

Ta kuma bayyana cewa, an ba da wannan tallafin ne domin samarwa mata marasa galihu da kuma habaka tattalin arzikinsu domin inganta rayuwar jihar.

Haka kuma, ta yi kira ga waɗanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da shi bisa ƙa’ida domin bunķasar tattalin arziƙinsu da cigaban su.

“Fatanmu shine inganta matan mu masu rauni ta hanyar samar da ayyukan yi a tsakanin su a jihar”, in ji ta

Gwamna Dauda Lawal a nasa jawabin, ya ce ƙarfafawa mata na daga cikin ajandar tattalin arziƙin gwamnatinsa don bunķasa ci-gabansu da ta iyalansu a jihar.

A cewarsa, sama da shekaru goma jihar na fama da matsanacin matsalar rashin tsaro, yana mai nuni da cewa yanayin ya jefa ɗimbin mata da dama zama zawarawa tare da samun ƙaruwar marayu, sannan ya yaba wa ofishin uwargidansa kan shirin tallafa wa mata da tallafin bunķasar ƙanana da matsakaitan sana’o’i.

By Babaji