Sojoji sun kashe ƴan ta’adda 60 a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’an Atisayen HAƊIN KAI sun yi nasarar kashe mayaƙan ƙungiyoyin ƴan ta’adda guda 60 a wata karanbatta a yankin Bita dake Jihar Borno.

A wata sanarwa da rundunar sojoji ta fitar a ranar Juma’a, ta ce hakan ya biyo bayan wani shiri ne na musamman da dakarun suka yi a ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan ta’addanci.

Harin ya fara ne da misalin ƙarfe 1:09 na dare a lokacin da mayaƙan suka farmaki sojojin Task Force na Birget ta 26, inda dakarun suka yi kwanton-ɓauna da yi musu ruwan wuta ta sama da ƙasa.

Kamar yadda rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce a yayin haka ne aka hallaka kimanin ƴan ta’adda 60.

Haka ma rundunar sojojin sama (NAF), ta ce dakarunta na Atisayen HAƊIN KAI ta yi gagarumar nasara akan mayaƙan Boko Haram.

Kakakinta, Air Commodore Ehimen Ejodame ya bayyana cewa, mayaƙan da dama sun rasa rayukansu a yayin karanbattar, wadda aka yi a sa’o’in farko na ranar 30 ga watan Mayu.

Ya kuma jaddada aniyar rundunar ta cigaba da bai wa Nijeriya kariya gami da kare al’ummar ƙasa masu ƙoƙarin kiyaye doka da oda, yana mai cewa ana ɗaukar matakan hana ayyukan ta’addanci tasiri a ko”ina a Nijeriya.

By Babaji