2026: INEC ta sanya ranakun zaɓukan gwamnonin Jihohin Ekiti da Osun

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta zaɓi ranakun 20 ga watan Yuni da 8 ga Agusta, 2026 a matsayin lokacin gudanar da zaɓukan gwamnonin Jihohin Ekiti da Osun.

Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana hakan a yayin rantsar da kwamishinonin zaɓe guda shida da majalisar dokoki ta tabbatar da su, ranar Juma’a.

Game da na Jihar Ekiti, ya ce za yi zaɓen ne a ranar 20 ga Yuni, 2026, a yayin da za a fara zaɓukan fidda gwani a ranar 20 ga watan Oktoban 2025 don bai wa jam’iyyu damar shigar da bayanansu ga shafin hukumar na musamman, wanda zai rufe a ranar 22 ga watan Disambar 2025.

Ya kuma ce, za a wallafa jaddawalin ƴan takara ne a ranar, sannan kuma a ranar 21 ga Janairu, 2026 ƴan takara za su fara yaƙin neman zaɓe acikin al’umma, wanda za a ƙarƙare sa’o’i 24 gabannin zaɓe.

Game da Osun kuwa, za a fara zaɓen fidda gwani ne a ranar 24 ga watan Nuwamba, 2025 kuma a gama a 15 ga Disamba.

Za a buɗe shafin shigar da bayanan ɗan takara ga jam’iyyu da misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar 9 ga Fabarairun 2026, wato kwanaki 180 gabannin zaɓe.

A ranar 11 ga Maris, 2026 ne za a fara yaƙin neman zaɓe, sannan kuma a dakatar kwana ɗaya kafin zaɓe.

Har’ilayau, Farfesan ya ce hukumar tana ƙoƙarin kammala shirye-shirye na zaɓukan cike gurbi na kujerun Majalisar Dokokin ƙasa da na jihohi.

By Babaji