Rundunar ‘yan sanda ta cafke matashin da ake zargi da yanka amarya a Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘yan sandan Kano ta tabbatar da cafke wani matashi mai suna Shu’aibu Abdulƙadir, mai shekara 35, wanda ake zargi da kisan wata amarya mai shekaru 22 a duniya.

Wannan na ƙunshe ne cikin wani jawabi da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Talata.

A ranar 6 ga watan Afrilun 2025 ne, Sha’aibu Abdulƙadir, wanda ke zaune a unguwar Maɗatai a Kano, ya kutsa cikin gidan wata amarya mai suna Rumaisa Haruna mai shekaru 22 da ke zaune a unguwar Tsamiyar Duhuwa a Kano, inda ya yi amfani da ɗan kwalin marigayiyar ya shaƙe ta, kuma daga baya ya daɓa mata wuƙa a wuya wacce ya ɗauko daga kicin ɗinta.

“Mijin Rumaisa mai suna Ibrahim Mohammed ne ya same ta cikin jini da mummunan rauni a wuya. Kuma bayan an kai ta asibiti ne aka tabbatar da cewa ta riga mu gidan gaskiya,” in ji Kiyawa, kakakin rundunar ‘yan sandan Kano.

A wata hira da rundunar ta yi da wanda ake zargi da kisan kan da kuma PREMIUM TIMES ta samu kwafinsa, Sha’aibu ya bayyana nadamarsa kan abin da ya aikata.

“Na yi nadamar abin da na aikata kuma ba abin da nake so idan an kai ki kotu kamar alkali ya yanke min hukuncin kisa kai tsaye ba zaman gidan yarin ba ko na samu salama.”

“Ba na son haɗuwa da ‘yan uwa saboda ban san da wane ido zan kalle su ba,” in ji Shu’aibu wanda ake zargi da kisan Rumaisa.

A cikin hirar da rundunar ta raba wa manema labarai, wanda ake zargin ya ba da labarin yadda aya aikata kisan da irin halin da ya shiga.

“Da farko ni sunana Sha’aibu Abdulƙadir kuma shekaruna 35. Ina zaune a cikin garin Kano a unguwar Maɗatai. Na shiga gidan Rumaisa ne da tsakar rana inda na yi amfani da ɗan kwalinta na shaƙe mata wuya kamar na minti 10. Bayan na sake ta har na juya zan fita, sai na ga alamun tana motsi.”

Sannan Shu’aibu ya cigaba da cewa, “Bayan na ga kamar tana motsi, sai na ji tsoron kar ta tashi asirina ya tonu. Shi ne na tafi kicin ɗinta na ɗauko wuƙa na daɓa mata a wuya na yanka ta ta gaba. Sai kuma na fice daga gidan.”

Ya kuma ce, “Kuma tun daga nan na kasa samun nutsuwa a rayuwata. Sai na tafi kan titin Mariri ina tsaye a wurin har zuwa wajen ƙarfe bakwai na Magriba saboda abin da na yi ya dame ni.”

Da yake bayyana dalilin aikata kisan kan, Shu’aibu ya ce, “son zuciya da son rai ne suka kai ni ga aikata kisan.”

Sannan ya tabbatar da cewa bai taɓa shaye-shaye ba kuma bai taɓa kisan kai a baya ba. Kuma wannan ne kisan kai karo na farko, domin “ban taɓa daukar wuƙa na yi wa wani rauni da ita ba,” ya faɗa.

Game da sana’arsa kuwa, Shu’aibu ya tabbatar wa da kakakin rundunar ‘yan sandan Kano cewa ba shi da wata sana’a. Sai dai yana koyon ɗinki kuma shi ɗalibi ne a Kwalejin koyon aikin ungozoma ta ɗan Shariff College of Nursing.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa irin kokarin da jami’ai masu binciken ƙwaƙwaf suka yi wajen kai wa ga kama wanda ake zargin.

Sannan ya ce bukaci al’umma da su riƙa bayar da rahoton duk abin da ba su gamsu da shi ba tare da jaddada aniyar rundunar ta cigaba da kare rayuka da duniyoyin da wanzar da zaman lafiya a jihar Kano.

Rundunar ‘yan sandan ta ce wanda ake zargin na tsare a hannunta kuma da zarar sun kammala bincike za su miƙa shi ga kuliya domin girbar abin da ya shuka.

By ukarofi