Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An yi kira gwamnati akan ta ƙara ƙaimi don ganin ana hukunta duk wanda aka kama da cin hanci da almundahana a ƙasar nan, hakan zai sa a ɗauki mataki na kawar da matsalar.
ɗansaran Kano, Alhaji Gambo Muhammad Danpass ne ya bayyana hakan ya ce duk wanda ya ga yadda ƙasar nan take tafiya na yawaitar samun rashawa da cin hanci amma rashin hukunta waɗanda ake kamawa na daɗa ta’azza lamarin ya zama wajibi a tabbatar ana hukunta wanda aka kama.
Ya yi nuni da cewa abin takaici a ƙasar nan tsohon Gwamnan Babban Banki a ce an samu gidaje guda sama da 700 banda irin tirilitoyin kuɗaɗen da ake zargin ya kwashe ya kamata a tsaya a tabbatar da doka da oda a ƙasar nan.
Ya ce kuɗaɗe da ake kwatowa a wajen masu wawure arziƙin ƙasa a tabbatar ana amfani da talakawa da su yadda za a inganta rayuwarsu ba kawai suma a rasa inda suke ba gara a fahimtar da mutane abinda ake yi da su.
Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ya ce babban abinda ake so a ƙasar nan shine tsarin bin doka da oda da hukunci ya tabbata akan duk wanda ya yi ba daidai ba komai girman muƙaminsa domin rashin yin hakan tafiyar makahon jaki za a riƙa yi.
Ya ce muddin za a cigaba da tafiya irin wannan ba za ta sauya zani ba don haka yana fata shugabanni su duba halinda ake ciki su nema mata mafita.
Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ya yi kira ga shugabanni akan su riƙe amana sai a kula da ita don a samu zaman lafiya a kuma kula da shari’a a kyautata harkar tsaro amma duk inda aka yi sakaci da waɗannan abubuwa to za a riƙa samun matsaloli.
