Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta amince da fitar da sama da Naira miliyan 150 domin sake gina masallacin Gadan da ke ƙaramar Hukumar Gezawa, wanda aka lalata a wani lamari da ya shafi wani matashi.
Kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida na jihar Kano, Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa gwamnati na cika alƙawarin da gwamnan jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ɗauka yayin ziyarar da ya kai wa al’ummar yankin.
A cikin ayyukan da gwamnati za ta aiwatar, ana kuma shirin gina makarantar Islamiyya, samar da sabbin ofisoshi, gyara banɗakuna, da kuma samar da wutar lantarki ta hasken rana tare da fanfunan tuƙa-tuƙa, domin inganta rayuwar al’ummar yankin.
Gwamnan ya buƙaci mutanen Gadan da su bada haɗin kai wajen tabbatar da nasarar aikin, tare da kula da sabon ginin bayan kammalawa.
Wannan shiri na ɗaya daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano na inganta wuraren ibada da kuma inganta ababen more rayuwa ga al’ummar jihar.
