Hukumar kwastom ta Nijeriya ta kama mota ɗauke da sinadaran haɗa bom

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumar Kwastom ta Nijeriya, reshen yankin Seme, ta kama wata mota da ake zargin tana ɗauke da kayan haɗa bom (IED).

Wannan na ƙunshe ne a wani bidiyo da hukumar ta wallafa a shafinta na ɗ, inda jami’anta ke binciken motar da aka kama a kan titin Legas zuwa Badagry.

An gano cikin motar akwai kwanso guda shida na ma’adani mai launin azurfa mai ɗauke da guba mai ƙarfi da aka fi sani da corrosiɓe mercury — wanda ake kyautata zaton ana amfani da shi wajen haɗa abubuwan fashewa.

Shugaban Kwastom na yankin, Kwanturola Ben Oramalugu, ya ce an kama mutum ɗaya da ake zargin yana da alaƙa da motar.

Ya bayyana cewa nasarar kama motar na nuna yadda Kwastom ke cikin shiri da kulawa wajen kare tsaron ƙasa.

Oramalugu ya ƙara da cewa wannan aiki na cikin matakan da Kwastom ke ɗauka don daƙile ayyukan fasa-ƙwauri da sauran laifuka a iyakokin Nijeriya.

Baya ga motar da ake zargin tana ɗauke da kayan haɗa bom, hukumar ta kuma kama wasu kayayyaki da dama da suka saɓa wa doka.

Kayayyakin sun haɗa da kuɗaɗen ƙasashen waje daga Birtaniya da Kanada, da Amurka da darajarsu ta kai kusan naira miliyan tara, wanda hakan ya saɓa dokar harajin kaya na waje.

Sauran kayayyakin da aka kama sun hada da robar ganyen wiwi guda 553 da buhunan shinkafar waje 1,415 da jarkokin man fetur guda 750, da kuma magungunan da ba a yi rijistarsu ba.

Kwanturola Oramalugu ya ce hukumar za ta miƙa kayayyakin da aka kama ga hukumomin da suka dace domin gudanar da bincike tare da ɗaukar mataki, da gurfanar da waɗanda ake zargi.

By ukarofi