Zamfara: Sarkin Ƙaura Namoda ya ba da shawarar gudanar da ƙirƙire-ƙirƙire da koyon sana’o’in hannu a makarantu 

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau 

Mai Martaba Sarkin ƙaura Namoda a Jihar Zamfara Alh. Sanusi Muhammad Asha ya yi kira ga makarantun gwamnati da masu zaman kansu da ke masarautarsa da su kara haɓaka shirin koyon sana’o’in hannu, kasuwanci da ƙirƙire-ƙirƙire a cikin manhajar karatunsu. 

Sarkin ya yi wannan kiran ne a ranar Talata a wajen bikin ranar yara ta ƙasa da aka gudanar a garin ƙaura Namoda hedikwatar ƙaramar hukumar ƙaura Namoda ta jihar. 

A cewarsa, ta hanyar samar da sabbin tsare-tsare da dabarun sana’o’in hannu domin amfanin ɗalibai zai taimaka wajen samar da guraben ayyukan yi a tsakanin ɗalibai bayan barin makarantunsu. 

Ya bayyana cewa shirye-shirye kamar sana’o’in gida, saka, saloon, yin sabulu, kafinta, walda, za su baiwa ɗalibai damar dogaro da kansu a ƙarshen karatunsu a matakin firmware da gaba da firamare. 

Sarkin ya ci gaba da bayyana cewa akwai buƙatar ɓullo da sabbin dabarun kasuwanci a matakin firamare da sakandare domin samar da ingantacciyar al’umma a nan gaba. 

“Ina kira ga hukumimin makarantun gwamnati da masu zaman kansu a makarantun firamare da sakandare a masarautata da su ƙara ƙaimi a annin dabarun kasuwanci, sana’o’in hannu a makarantunsu domin ci gaban zuriyarmu,” ya ce.

Basaraken ya buƙaci iyaye da su sanya ‘ya’yansu makaranta musamman ‘ya’ya mata domin samun nagartattun al’umma. 

A cewarsa, ta hanyar tarbiyyantar da yaro daya tamkar ka ilimantar da mutum daya ne amma ta hanyar ilimantar da ‘ya mace ɗaya tamkar ka ilmantar da al’umma gabaɗaya. 

Ya yabawa gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal bisa ayyana dokar ta-baci kan harkokin ilimi, inda ya ce masarautarsa za ta cigaba da bai wa gwamnati goyon baya don bunƙasa harkar ilimi a jihar.

By ukarofi