Hadiza Bala Usman ta ƙaryata BUA dangane da yarjejeniyar tashar jirgin ruwa ta Ribas

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan daidaita manufofi, Hadiza Bala Usman, ta ƙaryata zargin shugaban rukunin kamfanonin BUA, Alhaji Abdul Samad Rabiu, cewa an soke kwantiragin su na tashar jirgin ruwa ta Ribas ba tare da wani dalili ba. Ta bayyana hakan ne a martaninta ga wani rubutu da Rabiu ya wallafa, inda ya bayyana yadda aka soke kwantiragin su da NPA lokacin da take shugabanta.

Hadiza ta ce kamfanin BUA ya saɓa yarjejeniyar da suka ƙulla da hukumar tashoshin jiragen ruwa (NPA) tun kafin ta hau karagar shugabancin hukumar. Ta ƙara da cewa, kamfanin ya gaza fara gyaran layin Berths 5 zuwa 8 da aka buƙace su su gyara cikin kwana 90 bayan karɓar tashar a shekarar 2006, amma har bayan shekara 10 ba su fara gyaran ba.

A cewar Hadiza, an aika wa kamfanin da wasiƙar gargaɗi a ranar 11 ga Fabrairu 2016, kafin ta zama shugabar NPA, sannan aka sake aikawa da wata wasiƙar tunatarwa a ranar 17 ga Agusta 2016, amma duk da haka kamfanin ya ƙi cika sharuddan da aka gindaya musu. Ta bayyana cewa rashin cika wannan sharaɗi ya sanya soke kwantiragin su bisa ƙa’ida da doka.

Daga nasu ɓangaren, BUA sun taɓa bayyana a baya cewa soke kwantiragin ya saɓa da yarjejeniyar da ke tsakanin su da NPA, inda suka ce hukumar ce ke da alhakin gyara tashar da kuma zurfafa ruwan. Sun kuma ce sun garzaya kotu suka samu hukuncin dakatar da soke kwantiragin. Sun bayyana cewa lalacewar da aka samu a tashar na da nasaba da hare-haren ‘yan bindiga da suka lalata wasu sassa na ginin tashar.

By ukarofi