Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan ya faɗi haka a lokacin da yake ƙaddamar da buɗe manyan rijiyoyin burtsatse da gwamnatin ta gina a garin Katsina.
Ya ce unguwanni guda takwas ne suka amfana da rijiyoyin burtsatsen na zamani wanda za su samar da ruwan sha.
Unguwannin kuwa sun haɗa da Sabuwar Unguwa, Rahamawa/Abatuwa, Makera,bayan NYSC, Dutsen Safe da kuma rukunonin gidaje na Barhin da na asibitin gwamnatin tarayya.
Gwamnan ya bayyana cewa garin Katsina na fama da matsalar ruwan sha,tun “tsarin da akai na samar da ruwan daga madatsan ruwa na Kaiwa sama da shekaru 50 da suka wuce inji Dikko Raɗɗa.
Ya ƙara da cewa”tun daga nan ba a ƙara aikin faɗaɗa aikin samar da ruwan shan ba da wurin ake ruwa a cikin birnin Katsina”Inji gwamnan.
Malam Dikko Raɗɗa ya ce ganin yadda al’umma ke kwararowa zuwa birnin Katsina yasa gwamnatin sa ta gudanar da wannan aiki.
Gwamnan ya kuma sanar da cewa gwamnatin sa,ta sake ware Naira biliyan 25 domin sake bada aikin samar da ruwan sha a Katsina da wasu ƙananan hukumomi da ke jihar.
Ya kuma sanar da cewa a kasafin kuɗin 2025 gwamnatin jihar ta ƙara ware Naira biliyan 50 domin sake aikin samar da ruwan sha daga madatsar ruwa na Zobe zuwa ƙananan hukumomin Dutsinma,Ƙanƙara, Charanchi, zuwa wasu garuruwa da ke bisa hanya har zuwa Katsina.
