
Daga BELLO A. BABAJI
Kwamitin Majalisar Wakilai kan Ilimi a matakin farko da hukumomin jarrabawa ya ƙi sauraron tawaga daga Majalisar Kula da jarrabawa a yammacin Afirka (WAEC), ranar Juma’a.
Ƴan Majalisar sun ce shugaban WAEC na ƙasa ne kaɗai zai iya bada amsar tambayoyi game da matsalolin da ake samu a jarrabawar da ke gudana a yanzu.
Kwamitin ya bai wa WAEC sa’o’i 24 na ya amsa umarninsa na ya bayyana a gabansa a ƴan kwanakin nan.
Tawagar WAEC ƙarƙashin jagorancin babban mataimakin rajistira, Ambrose Okelezo ya bayyana cewa shugaban yana halin sanya ido ga harkokin jarrabawa sannan a ranar Litinin ne kaɗai zai iya zuwa.
Shugaban kwamitin Majalisar, Oforji Oboku, ya bai wa iyayen ɗalibai haƙuri game da tsaikon da ake samu a yayin jarrabawar.
Ya ce, lallai sai WAEC ta magance tsaikon da ake samu wajen shirya jarrabawar yadda ya dace.
Ya kuma yi tsokaci game da tantancewa ta komfuta, inda ya ce galibin makarantun ba su da na’urorin kwamfuta.
Daga ƙarshe, kwamitin ya bai wa shugaban na WAEC zuwa ƙarfe 2:00 na ranar Litinin da ya hallara a gabansa.
