Gwamnatin Katsina za ta ƙwace filayen da mutane suka mallaka ba bisa ƙa’ida ba

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamitin kula da dawo da gandun daji na Jihar Katsina yayi kakkausar gargaɗi tare da barazanar mataki na doka kan duk wanda ya mallaki fili a dajin Ɓarawa da ke ƙaramar hukumar Ɓatagarawa.

Shugaban kwamitin Hon Aminu Ashiru ƙofar sauri ya faɗi wa al’ummar ƙauyen Ɓarawa a wani sumame da ya kai a dajin Ɓarawan bayan samun ƙorafe-ƙorafe al’ummar ƙauyen.

Ya ce duka wani fili da aka ba wani daga shugabannin ƙananan hukumomi da hakimai da masu unguwanni ko wasu ,ba tare da izinin gwamnatin jihar ba ,an soke shi.

“Gwamnatin jihar Katsina ta kuma ƙwace filayen da aka bada ba bisa ƙa’ida ba nan take”inji shugaban kwamitin.

Hon Ashiru ƙofar bai ya bayyana cewa ba ƙauyen Ɓarawa ba kai duk faɗin jihar gwamna ne kawai ke da damar amincewa a ba wani fili a jihar.

Ya gargaɗi al’ummar jihar da su guji sayen filin gwamnati ba tare da sun ga takardar sahalewar gwamna ba.

By ukarofi