Al Nassr ta buƙaci Ronaldo ya ci gaba da zama a ƙungiyar

Spread the love

Daraktan wasannin Al Nassr, Fernando Hierro ya sanar a ranar Alhamis cewa suna yin iya ƙoƙarinsu domin Cristiano Ronaldo ya ci gaba da buga musu wasa

Ya faɗi hakan ne bayan wasu rahotannin da aka ce ɗan Portugal ɗin zai buga FIFA Club World Cup da za a fara daga 14 ga watan Yuni a Amurka.

A makon jiya Wydad Casablanca ta musanta batun da ake cewar ta ɗauki Ronaldo, domin ya ja ragamar ƙungiyar a Fifa Club World Cup a bana.

Ranar Litinin bayan da aka kammala gasar ƙwallon ƙafa ta Saudiyya, Ronaldo ya sanar a ɗ cewa, ”An rufe wannan babin.”

Hierro ya ce, ya ga saƙon, amma Ronaldo yana da sauran yarjejeniya da su zuwa ƙarshen watan Yuni, kuma suna iya ƙoƙarin ganin mai shekara 40 ya ci gaba da zama a Al Nassr.

Ronaldo shi ne kan gaba a gasar Saudiyya da ƙwallo 24 a raga, amma Al Nassr ta kasa samun gurbin shiga gasar zakarun Asia ta Champions League, bayan da ta yi ta uku a teburi.

Za a fara gasar FIFA Club World Cup, wadda aka sauya mata fasali daga 14 ga watan Yuni a Amurka, dauke da ƙungiya 32.

Lionel Messi zai buga gasar tare da Inter Miami da za su fafata da Al Ahly a filin the Hard Rock a Miami.

By ukarofi