
Daga BELLO A. BABAJI
Dakarun sojoji sun yi nasarar kashe kwamandan mayaƙan Boko Haram da ISWAP, wato Ami Abu Fatima, wanda akwai ladar Naira miliyan 10 akansa.
An hallaka shi ne a yayin wani atisayen jami’an a yankin Kukawa na Jihar Borno, kamar yadda rundunar sojoji ta wallafa a shafinta na X.
A ranar Alhamis ne aka gudanar da atisayen a ƙarƙashin tawagar ‘Operation HAƊIN KAI’ bayan samun bayanan sirri game da zirga-zirgar ƴan ta’adda a yankin.
A yayin haka ne rundunar ta ce, jami’anta na musamman suka hallaka Abu Fatima da mataimakinsa gami da wasu gomman ƙwararrun mayaƙan ƴan ta’addar.
Haka kuma an ruwaito cewa, Abu Fatima ya samu raunuka da dama gabannin mutuwarsa a yayin ba-takashi da sojojin.
A yayin haka ne sojojin suka ƙwato bindigogi ƙirar AK47 da mazubin alburusai da wasu kayayyakin haɗa ababen fashewa da dai sauransu.
Kazalika, rundunar ta tabbatar da cewa babu wanda aka rasa ko ya samu rauni daga ɓangaren dakarun tsaron, tana mai bayyana atisayen a matsayin gagarumar nasara nasar a ƙoƙarinta na daƙile ayyukan ta’addanci a shiyyar.
